IQNA

Taron Mabiya Addinai a Kasar Namibia

23:53 - February 18, 2018
Lambar Labari: 3482407
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron mabiya addinai a masallacin Quba babban birnin kasar Namibia.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Abul fadl Saburi babban dakaratn masallacin Quba a zantawarsa da iqna ya bayyana cewa, wannan taro zai guda a ranar 22 ga watan fabrairu, da kimanin karfe 14:30 zuwa 16:30 bayan zuhur.

Ya ci gaba da cewa, babbar manufar wannan taro dai ita ce samar da fahimtar juna  atsakanin dukkanin mabiya addinai da zaman lafiya da girmama juna.

Ya ce abin ban takaici ne yadda aka kirkiro kiyayya a saka a tsakanin mabiya addinai, ta yadda wasu suna gaba da juna da nuna musu tsananin kiyayya saboda rashin fahimta da ke tsakaninsu, wanda za a iya yin maganain hakan ta hanyar tattaunawa.

3692674

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha