IQNA

An Yanke Hukuncin Daurin Shekaru 5 Kan Nabil Rajab

22:49 - February 21, 2018
Lambar Labari: 3482415
Bangaren kasa da kasa, Kotun masarautar kama karya ta Bahrain ta daure shugaban cibiyar kare hakkokin bil adama a kasar Nabil Rajab shekaru biyar a gidan kaso.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarat cewa, Kotun masarautar ta yanke wannan hukunci ne a yau, bisa zargin Nabil Rajab da laifin rashin girmama kotu, da kuma yin kalaman batunci a kan wata kasa makwabciya.

Kotun ta ce Rajab ya yi rubutu a kan shafinsa na facebook tuna  cikin shekara ta 2015, inda ya yi bayani kan cin zarafin da fursunoni suke fuskanta a gidajen kason masarautar kasar, wanda a cewar kotun hakan ba gaskiya ba ne.

Baya ga Nabil Rajab, kotun masarautar kama karya ta kasar Bahrain ta yake wasu hukunce-hukuncen kisa a kan wasu matasa shida, bisa zargin cewa suna da shirin kashe babban hafsan hafsoshin sojin kasar.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suna ci gaba da yin Alah wadai da kakkausar murya a kan wadannan hukunce-hukunce na zalunci da kama karya da aka yanke a kan wadannan mutane saboda dalilai na siyasa, wadanda sun yi hannun riga da hakkokin bil adama da suke rayuwa a cikin wanann duniya, balantana a cikin kasarsu ta haihuwa.

3693493

 

 

 

captcha