Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na alakhbar.info cewa, an buga kur'anin mauritaniya da aka rubuta da hannu bisa kira'ar Warsh daga Nafiu, wanda shugaban kasar ya karba a shekara ta 2011.
A cikin shekara ta 2012 shugaba Muhammad Wuld bin Abdulaziz ya kaddamar da wannan kwafin kur'ani a wurin buda bakia cikin watan azumin Ramadan.
A halin yanzu an buga wannan kur'ani, kuma za ayada shi a tsakanin al'ummar kasar, wanda ake kiransa da kur'anin kasa, wanda gwamnatin kasar ta kaddamar da shia hukumance bisa kira'ar warsh wadda ake yi a kasar.
Ma'aikatar kula da harkokin addini takasar ce ta dauki nauyin dukkanin ayyukan buga kur'anin da kuma rarraba shi.