IQNA

Samar Da Kwafin Kur'ani Mai Rubutun Makafi A Masallatan Morocco

22:43 - February 23, 2018
Lambar Labari: 3482423
Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Morocco ta sanar da wani sabon shiri na samar da kwafin kur'anai masu rubutun makafi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na tanja24.com ya bayar da rahoton cewa, Abdulhayyi Galabzuri babban jami'in ma'aikatar kula da harkokin addini ta Morocco a yankin Tawan ya bayyana cewa, ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar da wani sabon shiri na samar da kwafin kur'anai masu rubutun makafi a dukkanin masallatan yankin.

Ya ci gaba da cewa, an ji ma da tunanin aiwatar da irin wannan shiri, kuma yanzu lokaci ya yi da za a aiwatar da shi, ta yadda za a wadata masallatai da kwafin kur'anai wadanda makafi za su iya karantawa.

Yanzu haka akwai wasu masallatai a yankin ad suke da irin wadannan kwafin kur'anai, amma adadinsu ba zai wadatar ba.

Haka nan kuam ya yi ishara da cewa, dukkanin wadanda suke da wata larura ta musamman wajibi nea  taimaka musu wurin samun sauki a dukkanin abubuwan da suke yi, kuma hanyar karatu da sanin addini na daya daga cikin wadannan hanyoyi.

3693853

 

 

 

 

 

captcha