IQNA

Jam’iayya Mai Mulki A Mauritania Ta Samu Nasarar Lashe Zaben Kasar

23:48 - September 09, 2018
Lambar Labari: 3482967
Bangaren kasa da kasa, jam’iyya mai mulki a kasar Mauritania ta samu nasarar lashe zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a makon jiya, yayin da jam’iyyar Islah ta masu kishin Ilama ta zo a matsayi na biyu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamafanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, shugaban hukumar zaben kasar Mauritania Muhammad Fal Wuld Balal ya sanar da cewa, jam’iyya mai mulki a kasar Mauritania ta samu nasarar lashe zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a makon jiya inda ta samu kujeru 67.

Haka nan kuma shugaban hukumar zaben ta kasar Mauritania ya ce, kimanin kashi 72.44 na dukkanin wadanda suka cancanci kada kuri’a ne suka jefa kuri’unsu a zaben.

A cikin mako mai zuwa ne dai za a gudanar da zaben zagaye na biyu, inda jam’iyya mai mulki za ta ara da sauran jam’iyyu domin samun sauran kujeru 22 da suka rage.

Jam’iyyun siyasa 98 suka shiga zaben na ‘yan majalisar dokoki da kuma na kananan hukumomi, inda a wannan karo har da jam’iyyun adawa sun shiga zaben, sabanin sauran lokutan baya.

3745109

 

 

 

 

captcha