Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Arakan ya bayar da rahoton cewa, a jiya an fuskanci matasalar komawar tawaga ta farko ta ‘yan kabilar Rohingya zuwa kasar Myanmar daga Bangaladesh kamar yadda aka tsara, saboda rashin zuwan wadanda suka kudiri aniyar komawa don kashin kansu.
An tsara a ranar jiya dukkanin ‘yan kabilar Rohingya da suke gudun hijira a kasar Bangaladesh da suke da nufin komawa Myanmar don kashin kansu da su hallara a bakin iyakokin kasashen biyu, babu wani daga cikinsu da ya hallara.
Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira akasar Bangaladeh Muhammad Abu kalam ya bayyana cewa, sun halarci yankin Kokas dake kan iyaka da Myanmar tun a safiyar jiya, amma babu wani daga cikin ‘yan gudun hijirar Rohingya da ya zo wurin.
Ya ce sun tanadi daruruwan motocin bas-bas domin jigilar ‘yan gudun hijirar zuwa Myanmar, bayan cimma matsaya kan hakan tare da hukumomin Myanmar, amma a halin yanzu wannan magana ta rushe.