IQNA

An Cafke Mutumin Da Ake Zargi Da Kusan Musulmi A Afrika Ta Tsakiya

20:27 - November 19, 2018
Lambar Labari: 3483133
Kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffukan yaki ICC ta tabbatar da cewa an mika mata mutumin nan da kotun take nema ruwa a jallo saboda zargin azabtarwa da kuma kashe musulmin kasar Afirka ta Tsakiya sannan kuma a halin yanzu tana tsare da shi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a wata sanarwa da kotun ta ICC ta fitar ta bayyana cewar jami'an kasar Afirka ta tsakiyan sun mika mata Alfred Yekatom wanda aka fi sani da Rambo a ranar Asabar din da ta gabata, sannan kuma ana ci gaba da shirye-shiryen gurfanar da shi a gaban kotun bisa wannan zargi na kisa da kuma azabtar da musulmin kasar da ake masa.

A ranar 29 ga watan Oktoban da ya gabata ne dai jami'an kasar Afirka ta tsakiyan suka kama Yekatom, wanda dan majalisa ne a kasar da kuma ci gaba da tsare shi bisa wannan zargi da ake masa.

Kwamitin binciken da MDD ta kafa ta gano cewa 'yan daban Kiristoci da suke karkashin jagorancin Yekatom din sun aikata ayyukan kisan gilla da laifuffukan yaki a kan musulmin kasar Afirka ta tsakiyan, don haka ne ma kotun ICC din ta fitar da sammacin kamo mata shi a ranar 11 ga watan Nuwamban nan kamar yadda babbar mai shigar da kasa a kotun ta ICC, Fatou Bensouda ta tabbatar.

3764900

 

 

captcha