IQNA

Musulunci Shi Ne Babbar Kariya Taimakekeniya Ita Ce Zata Jarya Takunkumi

23:41 - February 11, 2019
Lambar Labari: 3483363
Bangaren siyasa, shugaban kasar Iran Hojjatol Islam Hassan Rouhani ya gabatar da jawabi a ranar da jamhuriyar muslunci ta Iran  take cika shekaru 40 cur na nasarar juyin juya halin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Kamar yadda aka saba a ko wace shekara miloyoyin mutanen kasar ne suka fito gangami da jerin gwano na cika shekaru 40 da wannan nasarar a duk fadin kasar. 

A nan Birnin Tehran shugaban kasa Hujjatul Islam walmuslimin Dr Hassan Ruhani ne, ya rufe gangamin da muliyoyin mutane suka yi a dandanlin Azdi da ke nan tsakiyar birnin Tehran da jawabansa masu muhimmanci.

Da farko shugaban ya bayyana cewa kasar Iran ta yi rasa yankunanta a cikin daruruwan shekarun da suka gabata a hannun sarakunan masu rauni a gaban manya-manyan kasashen duniya na zamaninsu. Amma bayan nasarar Juyin juya halin musulunci kasar ta sami ci gaba a dukkanin bangaririn rayuwa da kuma matsayin a duniya da kuma yankin gabas ta tsakiya, tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba. 

Shugaban Ruhani ya tabbatar da cewa ba don juyin juya halin musulunci a Iran ya kasance na addinin musulunci ne ba, ba don juyin juya halin muslunci ya kasance na dogaro da Allah madaukakkin sarki, ba don juyin juya halin musulunci ya kasance na bin shari'ar musulunci da kuma shuwagabanni masu tsari daga iyalan gidan manzaon Allah  da kuwa juyin ba zai sami nasarar da ya samu ya zuwa yanzu ba. 

Da juyin da aka yi na yan kasanci ne da kuwa mutanen Iran ba zasu iya jurewa takurawar manya manyan kasashen duniya wadanda a duk tsawon tarihin kasar suna jujjuya kasar ba. 

A wani bangaren na jawabinsa, shugaba ruhani ya bayyana muhimmacin kasancewar tsarin shugabancin a kasar Iran ya kasance na jumhuriya islamiya. Don a ko wani shekara biyu mutane suna zaben shuwagabanninsu a akwatunan zabe, shuwagabanni kama daga jagoran juyin juya halin musulucin har zuwa ga shugaban kasa da sauran zabubbuka na majalisin kasa da na larduna. 

A bangaren makiya kuma shugaba Ruhani ya ce idan an ci gaba da samun hadin kai tsakanin mutanen da shuwagabannin kasar babu abinda many-manyan kasashen duniya zasu iya yi, kuma kasar iran zata ci gaba da samun ci gaba da daukaka a duniya.

3789199

 

captcha