Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, sheikh Muhammad Al-ush babban daraktan ma’aikatar kula da harkokin addini a lardin Sinai shi ma a nasa bangaren ya sanar da hakan, inda y ace a farkon watan Maris mai kamawa ne za a fara gudanar da gasar, wadda za ta zauki tsawon mako guda.
Haka nan ya kuma ya bayyana cewa, wanna gasa za ta kunshi bangarori daban-daban nagasar hardar kur’ani mai tsarki.
Duk kuwa da cewa dai wannan shi ne karon farko da za a gudanar da irin wannan gasa a mataki na lardin baki daya, amma tuni an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata a cewarsa.
Haka nan kuma an ayyana sunayen da suka yi rijista domin shiga gasar, wadda za ta samu halartar wakilai daga sassa na kasar ta Masar.