IQNA

Babban Malamin Kirista Na Mali Ya Jaddada Wajabcin Zaman Lafiya A Kasar

23:55 - July 03, 2020
Lambar Labari: 3484949
Tehran (IQNA) babban malamin mabiya addinin kirista a kasar Mali ya jaddada wajabcin zaman lafiya a tsakanin al’ummar kasar baki daya.

Shafin yada labarai na The Tablet ya bayar da rahoton cewa, Cardinal Jean Zerbo babban malamin mabiya addinin kirista na darikar Katolika a kasar Mali, ya bayyana cewa wajibi ne al’umma ta rn gumi zaman lafiya da juna matukar dai ana son ganin ci gaba a cikin rayuwa.

Wannan malamin kirista mai shekaru 76 a duniya wanda ya kai ga mukamin Cardinal a 2017, ya jaddada cewa musulmi da kirista dole ne su hada kai domin su yi a iki tare a dukkanin bangarori na ci gaban al’ummominsu, ba a Mali kawai ba, dukkanin kasashen Afirka da ma duniya.

Ya ce tun bayan zaben da aka gudanar a kasar Mali a kawanain baya, ga alama zaben ya bar baya da kura, wanda kuma sakamakon hakan ne kasar take neman fadawa cikin wani sabon rikici, ya ce yana kira ga dukkanin bangarorin siyasar kasar ta Mali da sun rungumi zaman lafiya da kuma hanyar tattaunawa domin warware matsalolinsu.

 

3908360

 

 

captcha