IQNA

Dattijo Mai Shekaru 107 Da Ke Zaune A Masallacin Manzon Allah (SAW) Shekaru Fiye Da 50 Ya Rasu

23:56 - June 20, 2021
Lambar Labari: 3486032
Tehran (IQNA) wani tsoho da yake zaune a masallacin manzon Allah (SAW) a mafi yawan lokutan rayuwarsa ya rasu.

Shafin yada labarai na albayan ya bayar da rahoton cewa, Sheikh Muhyiddin Hafizullah wanda ya kwashe fiye da shekaru 50 a kowace rana yana a cikin masallacin manzon Allah (SAW) a Madina, ya rasu yana da shekaru 107.

Wannan dattijo wanda dan asalin kasar Afghanistan ne, mahardacin kur'ani mai tsarki ne, mafi yawan lokutan rayuwarsa yana a cikin masallacin manzon Allah ne yana tilawar kur'ani mai tsarki.

Wannan ne yasa mutane suke kiransa da makwabcin masallacin manzo (SAW) wanda a kowane lokaci idan ya yi sallar asubah a  cikin masallacin, ya kan zauna a kusa da kabarin manzon Allah (SAW) yana karatun kur'ani, haka zai ci gaba da zama a cikin masallacin ko a harabarsa, har zuwa bayan kammala sallar isha'i.

Wadanda suka san shi sun tabbatar da cewa fiye da shekaru 50 da suka gabata haka yake rayuwarsa, inda a jiya Allah ya yi masa rasuwa yana da shekaru 107  a duniya.

3978746

 

 

captcha