IQNA

A daidai lokacin da akasarin kasashen duniya suka yi idi a yau wasu kuma sai gobe Talata

18:49 - May 02, 2022
Lambar Labari: 3487245
Tehran (IQNA) A yau ne akasarin kasashen musulmin duniya suke gudanar da bukukuwan idin karamar sallah

Galibin kasashen msuulmi dai sun sanar da yau a matsyin ranar idin karamar sallah, daga cikin kasashen da suka yi sallah a yau dai har da Saudiyya Masar  Aljeriya Najeriya da sauransu.

Wannan yana zuwa nea  daidai lokacin da wasu daga cikin kasashen musulmi suka sanar da yau Litinin a matsayin ranar 30 ga watan Ramadan, wato rana ta karshe a wanann wata mai alfarma, bayan da suka sanar da cewa ba su samu damar ganin jinjirin watan shawwala  a yammacin jiya Lahadi ba.

Daga cikin kasashen da suka sanar da Ranar gobe Talata a matsayin ranar idin karamar Sallah, har da kasar Iran, da kuam kasashen Pakistan, Bangaladesh, India da kuma Iraki.

Sai dai kuma tun a ranar jiya Lahadi wasu daga cikin kasashen musulmi sun yin sallar idi, bayan da suka ga watan a  yammacin Asabar da ta gabata, daga cikin kasashen kuwa har da Jamhuriyar Nijar, Jordan, Morocco da kuma Afghanistan.

 

4054314

 

 

captcha