A rahoton iqna, Wannan Kur'ani cikakke sassa 30 ne kuma ainihin rubutunsa ana ajiye shi a Taipei.
An buga da rarraba takaitattun adadi (kusan kwafi dubu) na wannan kur'ani a tsakanin musulmin kasar Sin a matsayin kyauta.
Wannan juzu'i na kur'ani yana da cikakken jerin ayoyi da batutuwa, kuma a karshensa akwai shafi kan fassarar wasu kalmomi na kur'ani a harshen Sinanci.
Wanda ake kira; Mai fassara alhazan Abdul Rahman Chan Ji Tavan ya mika wannan kwafin kur'ani ga Sheikh Khalid Tijoo, shugaban kungiyar musulinci ta kasar Sin a lokacin.