IQNA

Taron Maulidin Manzon Allah (SAW) a birnin Leicester na Ingila

16:07 - October 04, 2022
Lambar Labari: 3487953
Tehran (IQNA) Dubban al'ummar musulmi daga birnin Leicester na kasar Ingila ne suka gudanar da tattaki na maulidin Annabi Muhammad (SAW).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Leicester Mercury cewa, dubban al’ummar musulmi a birnin Leicester ne suka gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) a ranar Lahadi 10 ga watan Mehr.

Wannan tattakin da aka fara daga cibiyar musulinci ta Leicester dake kan titin Sutherland a Highfields da misalin karfe 13:00 na rana, an kammala shi da abincin rana a tsakiyar masallacin wannan birni. A cewar Mustafa Malik daya daga cikin wadanda suka shirya wannan bikin, mutane dubu takwas zuwa 10 ne suka halarci wannan bikin.

An shafe shekara 30 ana gudanar da tattakin duk shekara a birnin, amma Cllr Mustafa ya ce wannan ita ce babbar al'umma da ta taba gani. Ya ce: Mafi girman mutum a rayuwata da ta sauran musulmi shi ne Annabi Muhammad (SAW).

Ya ci gaba da cewa: "Don samun damar haduwa don murnar zagayowar ranar haihuwarsa tare da yada sakonsa na zaman lafiya ya sanya ni farin ciki sosai kuma yana da ban mamaki yadda mutane da yawa suka fito suna murna."

Roma Ali, dan majalisar birnin ma ta halarci wannan taron. Ya ce: “An yi fareti mai kyau, annashuwa tare da tutoci da yawa da lasifika da ke kunna kiɗa da waƙoƙi da yara da iyalai da yawa.

Har ila yau, 'yan sandan Leicestershire sun fitar da wata sanarwa da ke cewa: "Muna mika godiyarmu ga wadanda suka shirya tattakin na murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da kuma yadda suka yi hulda da 'yan sanda a kan wannan dadadden lokaci a kalandar Leicester.

Ba kamar sauran bukukuwan da ake yi a gida ba, musulmi suna gudanar da maulidin Manzon Allah a wuraren da jama'a ke taruwa.

4089631

 

 

captcha