IQNA

Marubuci Dan Qatar A Sashen IQNA A Baje Kolin Rubuce-Rubuce

23:31 - October 28, 2017
Lambar Labari: 3482046
Bangaren kasa da kasa, Saleh Garib shugaban bangaren al’adu na jarisar Alsharq ta kasar Qatar a sashen iqna a baje kolin rubuce-rubuce na kasa da kasa a Tehran.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ci gaba da gudanar da taron baje  kolin rubuce-rubuce na kasa da kasa da ake gudanarwa a Tehran an kasar, ya ziyarci sashen kamfanin dillancin labaran kur’ani na kasa da kasa wato IQNA a wurin baje kolin.

Wannan fitaccen dan jarida kuma marubuci dan kasar Qatar ya bayyana cewa, ya ji dadin ganin yadda wannan baje koli yake gudana, kuma ya karu da abubuwa daban-daban da bait aba yin tsammani ba.

Ya ci gaba da cewa, akwai hanyoyi da daman a aikin hadin gwaiwa tsakanin jaridar Al-sharq da kuma kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna, wanda a cewarsa za su taimaka wajen isa da sakonni al’adun muslunci da musulmi.

Haka nan kuma ya ui ishara da irin da irin rawar da kafofin yada labarai suke takawa wajen isar da sakonni da kuma yin tasiria cikin al’umma, inda ya ce haka lamarin a fuskar wayar da kan al’umma dangane da lamrra da suka shafi addini da kuma yada al’adun addini a tsakanin al’ummar msuulmi.

Daga karshe kuma ya nuna jin dadinsa akan yadda Iran ta bude wa Qatar dukkanin kofinta da kuma bata dukkanin taimako, a lokacin da kasashen larabawa suka kaaba mata takunkumi kuma suka haramta sayar mata da komai.

3657541


captcha