IQNA

Gina Makarantun Kur’ani Guda 21 A Kasar Senegal

22:22 - February 08, 2018
Lambar Labari: 3482376
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Senegal na da shirin gina makarantun kur’ani guda 21 a garin Kafrin da ke tsakiyar kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na almoslim.net cewa, shugaban kasar Senegal Macky Sal ya sanya hannu kan ware kasafin kudi na fara gina makarantu 18 a wannan gari.

Birnin kafrin dai ana yi masa lakabio da birnin ilimi a kasar Senegal, kasantuwar birnin ya shahara wajen yawan malamai na addinin muslunci a kasar tun daruruwan shekaru da suka gabata.

Maba ba babban daraktan ma’aikatar ilimi a wannan gunduma ya bayyana cewa, wadannan makarantu da za a gin aba za su takaitu da koyar da ilimin kur’ani ne ba kawai, har da ilimin zamani.

Kasar Senegal dai tana a yankin yammacin nahiyar Afirka ne, kum babban birnin kasar shi ne Dakar.

Kasar tana da tasiri a yammacin nahiyar Afirka da ma nahiyar baki daya, idan aka yi la’akari da irin rawar da take takawa a bangarori daban-daban na siyasa da suka shafi Afirka, kimanin kashi 93 cikin dari na mutanen kasar musulmi ne.

3689462

 

 

 

 

captcha