Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a daen yau ne za a gudanar da wani zaman taro mai taken tunanin Imam Khomeini (RA) a kan kur’ani mai tsarki a Senegal tare da halartar shugaban karaminin ofishin jakadancin Iran a kasar.
Wannan taro dai yana zuwa ne a daidai lokacin da aka gudanar da tarukan tunawa da cika shekaru ashirin da tara da rasuwar Imam a Iran da ma wasu kasashen duniya.
Marigayi Imam dai yana ganin kur’ani mai tsarki a matsayin tsarin rayuwa ga dukkanin musulmi, kuma yin aiki da koyarwasa shi ne mafita ga dukkanin matsalolin dan adam.