IQNA

Iran Za Ta Yi Aiki Tare Da Darikun Sufaye Domin Kara Tabbatar da Hadin Kan Musulmi

23:50 - July 07, 2018
Lambar Labari: 3482812
Bangaren kasa da kasa, jakadan Iran a kasar Seegal ya bayyana cewa Iran za ta hada karfi da karfe da darikun Sufaye a kasar Senegal domin kara tabbatar da hadin kai tsakanin musulmi.

 

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a lokacin da tawagar Iran karkashin jagoran Ainullah Qashqawi da kuma Hassan Ismati zuwa yankin Tuba birnin 'yan darikar Muridiyyah, Qashqawi ya bayyana cewa, kasantuwar mabiya darika mutane ne masu son addini da son manzon Allah da ahlul bait, ko shakka babu suna babbar gudunmawa da za su bayar wajen hada kan al'ummar musulmi.

Bayan na kuma sun ziyarci garin Kaulak na mabiya darikar Tijaniyya, inda a can ma suka gan ada Sheikh Ahmad Tijani Nyas shugaban darikar Tijaniyyah masu bin tafarkin faila.

Tattaunawar bangarorin biyu ta mayar da hankali ne kan wajabcin karfafa hadin kan al'ummar musulmi da kuma bin hanyoyi na ilimi domin wayar da kai kan hakiaknin musuluncin manzon Allah, wanda ya koyar da zaman lafiya a tsakanin al'ummomi.

3728281

 

 

آمادگی ایران برای همکاری با مدارس قرآنی سنگال

آمادگی ایران برای همکاری با مدارس قرآنی سنگال

 

 

captcha