Kamfanin dillancin labaran iqna, a nata bangaren Kungiyar ta kare hakkib bil'adama ta kasa da kasa ta ce; hukuncin ci gaba da tsare Nabil Rajab, babban abin kunya ne.
A bayanin da kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta fitar a yau Litinin ta ce; Daurin wasu karin shekaru biyar da aka yi wa mai fafutukar kare hakkin dan'adam Nabil Rajab, take adalci ne kuma abin kunya
Kungiyar ta kira yi gwamnatin kasar Bahrain da ta soke hukuncin ba tare da wani sharadi ba
Tun a ranar sha uku ga watan Yuni na dubu biyu da sha shida ne dai jami'an tsaron kasar Bahrain su ka kame Nabil Rajab wanda shi ne shugaban cibiyar kare hakkin bil'adama, saboda wata hira ta talabijin da ya yi.
Tun wancan lokacin har zuwa yanzu ana ci gaba da tsare da shi.
A yau Litinin ne wata kotu a kasar ta Bahrain ta yanke masa hukuncin zaman kurkuku na tsawon shekaru biyar
Kasar Bahrain ta fada cikin dambaruwar siyasa ne tun a cikin watan Febrairu na dubu biyu da sha daya saboda yunkurin al'ummar kasar na son ganin an kafa tsarin demokradiyya.