Kamfanin dillancin labaran iqna, Paparoma Francis yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda yake jawabi a gaban dubban masu sauraronsa a birnin Abudabi nna kasar Hadaddiyar daular laraba inda yake ziyarar aiki a can.
Paparoman ya kara da cewa akwai bukatar cocin catholika ta tashi tsaye don ganin a kauda wannan annobar wacce ta shafi fada-fada na wannan cocin a kasashen duniya da dama.
A wani bangare ya bukaci kiristoci da malaman cocin catholoca su kyautata halayensu don tabbatar da cewa an kawo karshen cin zarafin mata da yara a cikin cocin a dukkan kasashen da cocin yake da mabiya.
A jiya ne paparoman ya kammala ziyara mai tarihi wanda ya kai birnin Abu dabi na kasar Emmerate inda ya sami dimbin taba daga kiristoci mabiya mazhabar catholica a kasar, banda haka ya gana da malaman addinin musulunci da kuma sauran kananan addinai a kasar