IQNA

Kwamitin Fatawa A Sudan Ya Haramta Kulla Alaka Da Isra’ila

23:24 - October 01, 2020
Lambar Labari: 3485234
Tehran (IQNA) Kwamitin fatawa a Sudan ya fitar da bayanin da ke tabbatar da rashin halascin kulla alaka da Isra'ila.

Kwamitin ya sanar da wannan bayani ne a jiya bayan gudanar da zama da manyan malamai na fikihu mambobi a kwamitin suka yi ane a birnin khartum, inda suka bayyana cewa bai halasta kasar musulmi ta kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila ba.

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan da kasar Sudan ta nuna alamun karkata ga kulla alaka da yahudawan Isra’ila, sakamakon matsin lambar da take fuskanta kan hakan daga gwamnatocin Amurka, da kuma Saudiyya gami da UAE wadanda suke taimaka mata da kudade.

A cikin ‘yan makonnin da suka gabata ne gwamnatocin kasashen UAE da kuma Bahrain suka kulla alaka ta diflomasiyya da Isra’ila, lmarin da yake ci gaba da shan kakkausar suka daga al’ummomin kasashen larabawa da na musulmi.

 

3926562

 

 

captcha