Karatun kur'ani mai tsarki gaba daya a cikin watan ramadana ta zama wata dama ga mutane da yawa wajen sanin kur'ani mai tsarki a cikin wadannan shekaru.
Dangane da haka ne IQNA za ta rika sanya wani bangare na kur'ani mai tsarki a kowace rana a cikin watan Ramadan na shekara ta 2022 da muryar Malam Qasim Radi'i, malami kuma mai karatun kur'ani mai girma na duniya.