Karbala (IQNA) An gudanar da taron makoki na musamman ga yaran da ke halartar darussan bazara na hubbaren Imam Hussain a daidai lokacin da ake gudaar da tarukan Muharram.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, yaran da suka shiga wannan kwas sun nuna riko da wannan littafi mai tsarki ta hanyar rike kur’ani a hannayensu, sannan aka gudanar da zaman makokin Aba Abdullah al-Hussein (AS).