IQNA

Tsarin Kur’ani Na Digital A Hubbaren Imam Hussain (AS) A Karbala

22:33 - September 21, 2016
Lambar Labari: 3480799
Bangaren kasa da kasa, ana shirin samar da wani tsari na digital na kur’ani mai tsarki a hubbaren Imam Hussain (AS) a birnin Karbala.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama’a na hubbaren Imam Hussain (AS) cewa, bisa umarnin Sheikh Abdulmahdi Karbala’i za a fara gudanar da wannan shiri.

Shi dai wannan tsari zai kunshin lamurra da dama da suka hada da samar da yanayi wanda zai bayar da dama ga masu shafukan yanar gizo na hubbaren su iya samun kur’ani mataninsa da kuma nau’oin kir’a kyauta.

Kamar yadda kuma za a samar da kananan na’uroi da suke dauke da karatun da saut na digital ta yadda za su iya saita shi daidai yadda suke so da kuma irin bukatar da suke da ta, da hakan ya hada da sauraroro, ko takara, ko kuma harda.

Wila Safa tana daga cikin masu kula da tsarin, wadda ta bayyana cewa da zaran an kammala shi zai fara aiki ba tare da bata lokaci ba, kuma yanzu haka shirin ya riga yay i nisa, kuma ana fatan kammala shi a cikin kankanin lokaci a nan gaba.

Da dama daga cikin masu sha’awar lamurra da suka shafi karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta hanyoyi na digital wadanda ae amfani da sun a zamani.

Wannan hubbare mai tsarki na daga cikin cibiyoyin da suke aiwatar da ayyuka mas matuka amfani ta fuskar yada koyarwar kur’ani mai tsarki a kasar Iraki da kuma duniya ta hanyar yanar gizo.

3531792


captcha