IQNA

Musulmin Bellevue Sun Gudanar Da Zama Domin Tattauna Matsalar Kyamar Musulmi

16:55 - January 06, 2018
Lambar Labari: 3482275
Bangaren kasa da kasa, musulmin yankin Bellevue da ke birnin Washington na Amurka sun gudanar da zama domin tattauna hanyoyin kaucewa matsalolin da suke fuskanta.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bellevuereporter cewa, a jiya musulmin yankin Bellevue da ke birnin Washington na Amurka sun gudanar da zama domin tattauna hanyoyin kaucewa matsalolin da suke fuskanta daga masu kiyayya da musulmi.

Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da zaman ne tare da halartar wakilan kungiyoyin musulmi da kuma wasu daga cikin mazauna yankin gami da jami'an tsaro.

Babbar manufar gudanar da zaman dai ita ce tattauna lamurra da suka shafi musulmi a yankin, wanda kuma ake gudanar da irin wannan zama  a kowace shekara.

Bangarorin da suka halarci taron sun bijiro da shawarwari kan yadda za a fuskanci matsalolin kyamar msuulmi a yankin, inda akan samu wasu masu tsananin kyamar muuslmi da suke kai hare-hare ko kuma cin zarafin musulmi.

Hadin gwiwa a tsakanin kungiyoyin musulmi da kuma jami'an tsaro na yankin yana taimakawa matuka wajen bayar da kariya ga cibiyoyin muusmi, da suka hada da makarantunsu da cibiyoyinsu gami da masallatansu da suke a yankin.

3679499

 

captcha