IQNA

Gasar Kur'ani Ta Daliban Jami'a Hanya Ce Ta Bunkasa Al'adun Muslunci

22:44 - April 28, 2018
Lambar Labari: 3482611
Bangaren kur'ani, shugaban ofishin cibiyar ISESCO na yankin gabas ta tsakiya ya bayyana gasar kur'ani ta daliban jami'a musulmia matsayin wata dama ta bunkasa harkokin al'adun musulunci.

Gasar Kur'ani Ta Daliban Jami'a Hanya Ce Ta Bunkasa Al'adun MuslunciKamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Abbas Sadri shugaban ofishin cibiyar ISESCO na yankin gabas ta tsakiya ya bayyana gasar kur'ani ta daliban jami'a musulmia matsayin wata dama ta bunkasa harkokin al'adun musulunci a tsakanin matasa da ma sauran musulmi.

A yau ne aka shiga rana ta biyu a ci gaba da gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani ta duniya wadda ta kebanci daliban jami'a musulmi, wadda ake gudanarwa a birnin Mashhad na kasar Iran.

an fara gudanar da gasar ne a jiya Juma'a bayan kammala gasar kur'ani ta duniya a ranar Larabar da ta gabata a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran.

Wannan gasar dai ana gudanar da ita ne a karo na shida, tare da halartar daliban jami'a musulmi daga kasashe arbain da hudu  da suke karawa da juna.

Gasar dai ta samu karbuwa matuka daga dukkanin bangarorin da aka aikewa goron gayyata, kamadaga kasashen Asi'a da na Afrika gami da na turai.

Haka nan kuma cibiyoyin addini musamman cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi, inda wakilinta a yankin gabas ta tsakiya yake halartar taron gasar, wanda ya bayyana gasar da cewa, tana da matukar muhimmanci musamman kasantuwar ita kadai ce irinta da ake gudanarwa wadda ta hada daliban jami'a muuslmi daga kasashen duniya.

3709603

 

captcha