IQNA

Rauhani Ya Ce Da Johnson: Idan Da Babu Qasim Sulaimani Da Ba Ku Cikin Aminci

23:44 - January 10, 2020
Lambar Labari: 3484401
A zantawar da ta gudana tsakanin shugaba Rauhani da firayi ministan Birtaniya ya bayyana matsayin shahid Sulaimani.

Kamfanin dillancin labaran IQA, a cikin wata zantawar wayar tarho da ta gudana tsakanin shugaba Rauhani da firayi ministan Birtaniya, Rauhani sheda masa cewa, in da babu Qasim Sulamini to ba ku kasance cikin aminci ba.

Shugaba Rauhani ya shedawa Boris Johnson cewa, Iran ba za ta amince da kalaman da wasu daga cikin jami’ain gwamnatin Birtaniya suka yi ba kan kisan shahid Kasim Sulaimani.

Haka nan kuma ya bayyana matain da Iran ta dauka mayar da martani da manyan makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka a Iraki da cewa, hakan ya yi daidai da ayar doka ta 51 ta majalaisar dinkin duniya, wadda ta bayar da dama ga kowace kasa da mayar da martani domin kare kanta.

Shugaba Rauhani ya shedawa firayi ministan Birtaniya lokaci ya yi da ya kamata kasashen turai s zama masu ‘yancin siyasa, maimakon ci gaba da zama ‘yan amshin shata ga Amurka, inda suka zama tamkar rakumi da akala, duk inda Amurka ta kada nan suka nufa.

Shi ma a nasa bangaren firayi ministan kasar ta irtaniya Boris Johnson ya bayyana fatar ganin an samu kwaciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya, da kuma kai zuciya nesa tsakanin Amurka da Iran, kamar yadda ya jaddada cewa kasarsa za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran.

https://iqna.ir/fa/news/3870436

 

captcha