IQNA

An Daure Matar Da Keta Alfarmar Kur’ani Watanni 6 A Gidan Kaso A Tunisia

16:44 - July 15, 2020
Lambar Labari: 3484986
Kotun kasar Tunisia ta yanke hukuncin daurin watanni shida a gidan kaso a kan Amina Saharqi kan keta alfarmar kur’ani mai tsarki.

Shafin yada labarai na jaridar watan ta kasar Tunisia ya bayar da rahoton cewa, kotun kasar ta Tunisia ta yanke hukuncin daurin watanni shida a gidan kaso a kan Amina Saharqi ne, bayan samun ta da laifin yada kiyayya da tozarta abubuwa na addini masu daraja da tsarki.

Babban mai shigar da kara na kotun ya bayyana cewa, an yanke wa Amina Sharqi wannan hukunci ne bayan tabbatar da laifukan da ake zarginta, sannan kuma za ta share watanni shiga a garkame a gidan kaso, baya ga haka kuma za ta biya tara da dinar dubu biyu, kwatankwacin euro 650.

Amina Sharqi dai yada wani rubutu a shafukan yada zumunta da ta kira shi da suratu corona, tana mai izgili da surorin kur’ani mai tsarki, lamarin day a harzuka mutane a kasar.

Bayan faruwar lamarin ne jami’an ‘yan sanda suka gayyace domin amsa tambayoyi, daga nan kuma jami’an tsaron suka  yi awon gaba da ita.

 

3910663

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tambayoyi amsa gayyace harzuka faruwar addini
captcha