IQNA

Martanin Kungiyar Kasashen Musulmi Kan Kone Kur'ani A Sweden

20:54 - August 31, 2020
Lambar Labari: 3485137
Tehran (IQNA) Kungiyar kasashen musulmi OIC ta mayar da kakkausan martani dangane da kona kwafin kur’ani mai tsarki a kasar Sweden.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta fitar, ta bayyana kona kur’ani mai tsarki da aka yi a kasar Sweden na a matsayin wani sabon yunkuri na nuna tsananin kyama da gaba ga addinin muslunci.

Bayanin ya ce irin wannan mataki ba a bu ne da zai haifar da zaman lafiya a duniya ba, a kan haka ya zama wajibi kan gwamnatocin da ake aikata haka a cikin kasashen su gaggauta daukar matakan hana sake faruwar irin haka, tare da kamo dukkanin wadanda suke da hannua cikin wannan aika-aika a gurfanar da su a gaban kuliya domin su fuskanci hukunci.

Ita ma a nata bangaren cibiyar Ahhar a kasar Masar ta fitar da nata bayanin, wanda yin tir da Allawadai da kakausar murya kan wanann mummunan aiki.

A daya bangaren kungiyoyin musulmi da ma fitattun mutane a duniya suna ci gaba da mayar da martani kan wannan aiki na tsokana da masu tsananin kiyayya da musulmi suka aikata a Sweden, da kuma tunzura sauran masu akida irin tasu a kasashen turai domin su aikata hakan, inda lamarin ke shan kakkausar suka da Allawadai, da kuma neman a dauki mataki a kan masu aikata hakan.

3919933

 

captcha