IQNA

Sayyid Nasrullah: Amurka Ta Yi Ta Kokarin Ganawa Da Hizbullah Amma Har Yanzu Hakan Ba Ta Samu Ba

16:20 - February 09, 2022
Lambar Labari: 3486928
Tehran (IQNA) babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, Amurka ta yi ta kokarin ganin  ta gana da kungiyar Hizbullah a lokuta daban-daban.

A zantawarsa da tashar alalam a daren jiya Talata, babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, Amurka ta yi ta kokarin ganin  ta gana da kungiyar Hizbullah a lokuta daban-daban, amma har yanzu hakarta ba ta cimma ruwa ba.

Ya ce babban abin da Amurka take bukata shi ne, Hizbullah ta yi watsi da alakarta da Iran, ta kuma daina taimaka wa Falastinawa, wanda kuma wadannan abubuwa ne da ba za su yiwuwa, kuma kin amincewa da sharuddan Amurka da Hizbullah ta yi, shi ne babban abin da yasa ake yin matsin lamba kan kasar Lebanon.

Baya ga haka kuma Sayyid Nasrullah ya ce, a lokuta daban-daban Amurka ta sha yi wa Hizbullah tayin darurun miliyoyin daloli, amma Hizbullah tana yin watsi da hakan, domin kuwa ta san manufar hakan ita ce kokarin dana tarko domin samun damar raunana karfin kungiyar.

Dangane da barazanar yakin da Amurka take yia  kan Iran, ya ce wannan magana ce ta fatar baki, domin kuwa da hakan zai yiwu cikin sauki, da tuni Amurka ta aiwatar, amma saboda sanin cewa Iran ba kamar sauran kasashen larabawa da Amurka ta raina ba ce, wannan ne yasa take taka tsantsan.

4034980

 

captcha