IQNA

Sallar Juma'a ta farko ta watan Ramadan a masallacin Al-Aqsa tare da halartar dubun-dubatar Falasdinawa

18:34 - April 08, 2022
Lambar Labari: 3487141
Tehran (IQNA) An gudanar da sallar Juma'a ta farko ta watan Ramadan a masallacin Al-Aqsa, duk da tsauraran matakan da 'yan sandan gwamnatin sahyoniyawan suka dauka, tare da halartar Palasdinawa sama da dubu 80.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Ahd cewa,

duk da tsauraran matakan tsaro na soji da gwamnatin sahyoniyawan ta dauka na takaita zirga-zirgar masu ibada zuwa masallacin Aqsa, dubun dubatar Falasdinawa sun gudanar da sallar Juma'a ta farko a watan Ramadan a cikin ginin masallacin Al-Aqsa da kuma harabarsa.

Ofishin kula da harkokin addini a Falasdinu ya yi kiyasin cewa sama da masu ibada dubu 80 ne suka yi salla a alkiblar musulmi ta farko a wannan juma’a, wadanda suka fito daga yankunan da aka mamaye a shekara ta 1948, wato Kudus da yammacin gabar kogin Jordan.

Domin takaita yawan masu ibada a masallacin Al-Aqsa sojojin yahudawan sahyoniyawan sun rufe dukkan tituna da kuma unguwannin da ke kusa da tsohon birnin Kudus da sanyin safiya, lamarin da ya tilastawa dubban masu ibada yin tafiya mai nisa don isa masallacin. 

Dubban 'yan sandan yahudawa ne da kuma wadanda ake kira "masu tsaron kan iyakoki" aka jibge a kofar tsohon birnin, da kuma kan titunan da ke kan hanyar zuwa masallacin Al-Aqsa, kuma sun kafa shingayen binciken ababen hawa da yawa a kan dukkanin tituna da ke isa masallacin.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4047727

captcha