IQNA

An kafa wurin buga kur'ani a kasar Kuwait

21:24 - December 23, 2022
Lambar Labari: 3488384
Tehran (IQNA) Kakakin kungiyar masu sha'awar buga kur'ani mai tsarki da sunnar ma'aiki ta kasar Kuwait ya sanar da kammala aikin gudanar da ayyukan buga kur'ani mai tsarki na "Sheikh Nawaf Ahmad" a kasar.
An kafa wurin buga kur'ani a kasar Kuwait

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-Rai a kasar Kuwait cewa, Mubarak Salem Al-Hyan kakakin hukumar da’awar kur’ani da sunnar ma’aiki ta kasar Kuwait ya sanar da cewa, wannan kungiya tare da hadin gwiwar ma’aikatar kwadago ta kasar Kuwait ta sanar da cewa; ya kammala aikin zayyana majalissar da'ar Alqur'ani ta Sheikh Nawaf Ahmad, kuma an fara daukar matakan shari'a don aiwatar da shi.

Ya kara da cewa: Kungiyar masu sha'awar buga kur'ani da hadisai na ma'aiki ta tsara aikin wannan majalissar don ya zama wani babbar fasaha mai kima da cancantar fasahar buga kur'ani.

Al-Hyan ya ci gaba da cewa: Wannan aikin yana cikin yankin masana'antu na "Sobhan" kuma a kan wani fili da ya kai dubu 27,200, kuma zai hada da dakunan kasa guda biyu, wanda na farko shi ne wurin ajiye motoci da kuma ajiyar albarkatun kasa, da kuma na biyu shi ne shigar da na'urorin sanyaya iska na ginin.

Ya kuma ce: Ginin gudanarwa na majalissar da dakin taro (wajen karbar baki), babban gidan buga littattafai da masallaci za su kasance a kasa, kuma a bene na daya zai hada da babban ofishi da ofisoshi masu alaka da majalissar.

 

 

4108957

 

Abubuwan Da Ya Shafa: buga kasar Kuwait littafai fasaha majalisa
captcha