IQNA

An rufe ofishin jakadancin Sweden a Bagadaza

13:59 - July 20, 2023
Lambar Labari: 3489507
Bagadaza (IQNA) Ofishin jakadancin Sweden a Iraki ya sanar da cewa zai dakatar da ayyukansa a Bagadaza har sai wani lokaci.
An rufe ofishin jakadancin Sweden a Bagadaza

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ofishin jakadancin kasar Sweden a Iraki ya sanar da dakatar da ayyukansa a birnin Bagadaza har sai an sanar da hakan.

Ministan harkokin wajen Sweden Tobias Blaström ya ce mahukuntan Iraki sun gaza wajen gudanar da ayyukansu na kare ofisoshin diflomasiyya, kuma harin da aka kai ofishin jakadancin Sweden a Bagadaza abu ne da sam ba za a amince da shi ba.

Ya ce: Mahukuntan Iraki sun gaza wajen gudanar da ayyukansu na ba da kariya ga ofisoshin diflomasiyya.

A gefe guda kuma, a daidai lokacin da ma'aikatar harkokin wajen Sweden ta rufe ofishin jakadancinta da ke Bagadaza, ta kuma gayyaci jakadan Iraki da ke Stockholm.

A sa'i daya kuma, an sanar a birnin Bagadaza cewa, ana gudanar da wani muhimmin taro karkashin jagorancin firaministan kasar Iraki Muhamad Shi'a al-Sudani, domin nazarin matsayin kasar nan dangane da wulakanta kur'ani mai tsarki.

A safiyar yau mutane da dama ne suka shiga harabar ofishin jakadancin Sweden inda suka kona ginin ofishin jakadancin.

Wannan matakin dai na nuna adawa da yarjejeniyar da 'yan sandan kasar Sweden suka yi na gudanar da wani gangami a wajen ofishin jakadancin Iraki da ke Stockholm domin kona wani kur'ani.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa da sanyin safiyar Alhamis din nan daruruwan masu zanga-zangar ne suka shiga ginin ofishin jakadancin kasar Sweden inda suka kona shi.

 

 

4156548

 

 

captcha