IQNA

Sayar da kwafin Kur'ani da aka yi wa ado na Caucasian a baje kayan fasahar Musulunci

18:25 - April 12, 2024
Lambar Labari: 3490974
Za a siyar da wani kur’ani da aka kawata daga yankin Caucasus kan kudi fan 60,000 zuwa fam 80,000 a wani a baje kayan fasahar Musulunci

A cewar Al-Yum Al-Sabi, wajen baje kayan gwanjo na kasa da kasa na Sotheby ya kaddamar da wani gwanjon sayar da kayan fasahar musulunci na duniya wato"Arts of the Islamic World". Wannan gwanjon ta kunshi tsofaffin ayyukan addinin musulunci da dama kamar su Al-Qur'ani mai girma, tsofaffin litattafai da kayan tarihi da aka kawata.

Daga cikin kayayyakin da aka bayar domin sayarwa akwai wani babban  kur’ani mai girma da aka yi wa ado, wanda Muhammad bin Saleh al-Kumi ya shirya a shekarar 1846-1847 a yankin Gabashin Caucasus na Dagestan, kuma farashinsa ya kai fam 60,000 zuwa 80,000.

Baya ga takardun da aka tanadar don wannan rubutun, wannan kur'ani yana nuna muhimman abubuwan da ke tattare da kur'ani da aka samu a yankin Dagestan.

Wadannan Al-Qur'ani an bambanta su da yawa da kayan ado masu launi. A cikin bincikensa na kur'ani mai alaka da Dagestan a cikin dakin karatu na Burtaniya, Gallup ya lura da cewa ginshikin wannan kur'ani ana yawan yin shi da tambarin hannu da launi da ake iya gani a gefen wannan kur'ani.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4209919

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kur’ani kwafi kayan tarihi musulunci fasaha
captcha