Bangaren kur’ani, an gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Rasha wadda ta samu halartar wakilan cibiyoyin muslunci na kasar da kuma makarantun kur’ani inda aka kammala gasar bayan kwashe kwanaki takwas ana gudanar da ita.
2012 May 28 , 20:41
Bangaren kasa da kasa; maikel Guvo ministan da ke kula da harkokin da suka shafi ilimi da koyarwa a kasar Britaniya ya bayyana cewa:raba kur'ani a makarantu babu wata matsala musamman da sunan taimakawa wajan yada wannan littafi mai tsarki da yada addini a makarantun.
2012 May 28 , 16:57
Bangaren kur'ani, an gudanar da gasar karatun kuran mai tsarki a kasar Thailnd wanda musulmi mazauna garin Yal suka dauki nauyin shirayaw ada gudanarwa tare da haltar malamai da kuma daliban kur'ani da suka gudanar da karatuttuk da kuma harda.
2012 May 26 , 22:54
Bangaren da ke kula da harkokin kur'ani: mai kula da shirya gasar karatun kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran yayi nunida shirya gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa a tsakanin yan jami'a musulmi da cewa: ta hanyar gudanar da irin wannan gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa a tsakanin yan jami'a musulmi muna iya samar da wani juyin juya halinm na al'adu a tsakanin yan jami'a.
2012 May 23 , 13:04
Bangaren kasa da kasa; Muhammad Huseini Hashimi mai kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta iran a Hadeddiyar daular larabawa ya bayyana cewa makaranci guda ne daga Uran zai halarci gasar karatun kur'ani mai girma da tafsirinsa ta kasa da kasa da ake gudanrwa duk shekara a birnin Dubai cibiyar kasuwancin hadeddiyar daular larabawa.
2012 May 23 , 13:03
Bangaren kur'ani, ana samun ci gaba wajen kafa cibiyoyin addinin muslunci da na kur'ani a kasar Brazil wanda musulmi mazauna kasar waanda akasarinsu sun fito ne daga kasashen larabawa suke kafawa domin amfanin mabiya addinin muslunci da ke kasar.
2012 May 22 , 20:44
Bangaren kasa da kasa;A wannan litinin din daya ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya a jami'ar ilimi da lura da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma za a gudanar da wani zama na bincike da neman kawo gyara a cikin tarjamomin da ake yin a kur'ani mai girma a cikin yarukan Spaniyanci da Hausa da mu'assisar tarjamarWahayi ta ke gudanarawa .
2012 May 20 , 16:35
Bangaren kur’ani mai tsarki, an bude ajujuwan koyar da tafsirin kur’ani mai tsarki a husainiyyar baqiyatollah da ke birnin zaria a arewacin tarayyar Nigeria da nufin fara shirin fuskantar lokacin azumi mai zuwa wanda dukkanin musulmi suke sauraron karatu da tafsirin kur’ani mai tsarki a fadin kasar.
2012 May 19 , 14:42
Bangaren kasa da kasa; Muhammad Mursi dan takarar neman shugabancin kasar Masar a zaben shugaban kasa karkashin inuwar kungiyar Ikhwanul musulmin a kasar masar ya bayyana cewa: sabon kundin tsarin mulki da dokokin da a za diogara das u za su dogara ne da kur'ani mai girma .
2012 May 14 , 15:39
Bangaren kasa da kasa; a sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar da kuma wadda mu'assisar gudanar da ayyukan da suka shafi bincike da nazarin jin ra'ayin jama'a ta PEW a kasar Amerika ta fitar yayi nuni da cewa: kaso satin da shida cikin dari na al'ummar kasar masar sun bukaci kafa gwamnati da dokokinta suka dogara da asasin koyarwa ta kur'ani da addinin musulunci.
2012 May 14 , 15:39
Bangaren kasa da kasa; sakamakon wani bincike da aka gudanar a wata cibiya ta kwararru kan binciken masu sauraron gidajen radiyoyi a kasar Marokko ya fitar da samakon bincikensa da a ciki ya bayyana cewa daga cikin gidajen radiyoyi da ake saurara a wannan kasa ,radiyon kur'ani ne yafi yawan masu saurare da hakan ke nufin cewa yawancin al'ummar kasar na yin riko da addinin musulunci ne kuma ana kara samin masu ra'ayin addini da riko da addinin musulunci da kuma kur'ani a wannan kasa.
2012 May 12 , 17:11
Bangaren kasa da kasa; a wani taron manema labarai da aka gudanar kan rawar da mahardata kur'ani mai girma ke takawa a lamuran da suka shafi ci gaban zamantakewa a tsakanin kasashen Chadi da kamaru an bayyana cewa daga farkon daya zuwa hudu ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya da muke ciki a garin Injamaena za a gudanar da taron kan wannan lamari.
2012 May 12 , 17:10